Muhammad mansur ibrahimDownload 318.36 Kb.
Page1/5
Date18.06.2018
Size318.36 Kb.
  1   2   3   4   5
من هم أحباب أهل البيت؟

بلغة الهوسا

تأليف محمد المنصور إبراهيم

SU WANE NE

MASOYAN

AHLUL BAITI ?
WALLAFAR :

MUHAMMAD MANSUR IBRAHIM

SOKOTO
FASSARAR:

ALIYU RUFA’I GUSAU

Bugawa da Yaxawa:

Mu’assatu Ahlilbaiti Wassahabah, Nigeria

(C) 2005

ABUBAWAN DA KE CIKI

Godiya

Sadaukarwa

Gabatarwar Mai fassara

Gabatarwar Mawallafi
BABI NA XAYA

1.0 Iyalan Gidan Manzon Allah (SAW)


  1. Ma’anar Iyalan Gida

  2. Dangogin Manzon Allah (SAW):

  3. Babannin Manzon Allah (SAW) da Gwaggonninsa (‘Yan uwan Haihuwar Mahaifinsa)

  4. Yanne da Qannen Manzon Allah (SAW) maza da mata (‘ya’yan ‘Yan uwan Mahaifinsa.

  5. Kawunnen Manzon Allah (SAW) da Innoninsa (‘Yan uwan Haihuwar Mahaifiyarsa maza da mata

  6. Matan Manzon Allah (RA)

  7. Ya’yan Manzon Allah (SAW) Maza da Mata


BABI NA BIYU

2,0 Martabobin Ahlulbaiti

  1. A cikin Al-qur’ani

  2. A cikin Hadisi (Sunna)

  3. Haqqoqin Ahlulbaiti akan Musulmi


BABI NA UKU

3.0 Alaqar Magabata da Ahlulbaiti

3.1 Matsayin Ahlulbaiti a wurin Magabata

3.2 Auratayya Tsakanin Ahlulbaiti da Sahabbai da Tabi’ai
BABI NA HUXU

4.0 Ahlulbaiti a wurin Rafilawa

4.1 Su wane ne Ahlulbaiti a wurinsu?

4.2 Sun raba xaya Biyu
BABI NA BIYAR

5.0 Matsayin Ahlulbaiti game da Rafilawa (‘yan Shi’ah)

5.1 Matsayin Ali Xan Abu Xalib (RA)

5.2 Matsayin Hassan Xan Ali (RA)

5.3 Matsayin Hussaini Xan Ali (RA)
5.4 Matsayin sauran Ahlulbaiti

5.5 Bukukuwan Ashura

5.6 Naxewa.

GABATARWAR MAI FASSARA
Yahudawa da Nasara, maqiya addinin Musulunci, sun yi qoqarin saqa tunanin ‘yan Shi’ah, da gwada mu su cewa addinin musulunci addini ne na ‘yan gidanci. Saboda haka sai suka taqaita shugabancin al’umma – wanda aka san shi a matsayin Shawara tsakanin musulmi – su ka mai da shi haqqi ga iyalan gidan Manzon Allah Ahlulbaiti”. To da ma abin ya tsaya nan, da sauqi. Sai kuma daga cikin iyalin na Manzon Allah (SAW), suka ware wasu, suka ce ba da su ba a ciki. Abin kuma bai tsaya ga wariyar ba, sai kuma suka bi su da, bi-ta-da-qullin sukar lamiri da tozartawa, su na jifarsu da qazafi da miyagun lafuzza.

A cikin xan wannan littafi, Malam Muhammad Mansur Ibrahim Sakkwato, ya yi qoqarin fexe wa mai karatu biri har wutsiya, game da waxanda ke iya shiga qarqashin tutar iyalan gidan Manzon (SAW). Ya kuma bayyana irin darajoji da suka kevanta da su. Sa’annan ya ba da haske game da matsayin Ahlul Sunnah da na ‘yan Shi’ah akansu ta yadda, mai karatu zai iya yanke hukunci da kansa “Su wane ne Masoyan Ahlulbaiti”?

Malam Mansur ya yi amfani da ayoyin Al-qur’ani mai girma da Hadissai ingantattu da tatattun bayanai na tarihi, don gamsar da mai karatu da ingancin hujjarsa. Ya kuma yi adalcin mayar da ko wace magana zuwa ga mai ita daga marubutan Sunnah da na Shi’ah baki xaya. Wannan littafi zai taimaka matuqa wajen gane bakin zaren abinda ya shafi Ahlulbaiti da masoyansu, musamman ga matasa masu kishin musulunci.

Na samu wannan xan littafi nasa rubuce ne da larabci duk da yake ya gabatar da shi da Hausa a matsayin Lacca a wurare daban daban. A zatona samun wannan littafi da Hausa a wannan qasa tamu yafi alfanu bisa ga kasancewarshi da larabci. Don haka na yi gaggawar yin wannan aiki na fassara shi zuwa harshenmu na Hausa. Da fatar Allah ya ba ni ladar da ke ciki, ya sa kuma mu cimma manufar da mu ka dosa.

Allah Ya yi mana jagora, Amin.

Aliyu Rufa’i Gusau

Sashen Tsare-Tsare, Bincike da

Qididdiga.

Ma’aikatar Lamurran Addini ta

Jihar Zamfara.
Gabatarwar Mawallafi

Bayyanar aqidar Shi’a a Najeriya ta arewa ya zo ne bayan juyin juya halin da aka yi a Iran a qarqashin jagorancin Ayatullahi Khumaini a shekarar 1979. Kafin wannan lokaci dukkan musulmi a wannan yanki, su na bisa ga turbar Sunnah ce wadda Mujaddadi Usmanu xan Fodiyo (Allah ya qara ma sa rahama) ya sabunta.

A bisa ga wannan turba, dukkan musulmin wannan qasa su na mutunta iyalan gidan Manzon Allah (SAW) tare da Sahabbansa. Alal Misali, ba za ka iya qirge masu sunan Fatima ba, haka ma Hassan da Hussaini a gidajen Musulmi a wannan qasa. Haka nan masu xauke da sunayen matayen Manzon Allah (SAW) kamar su Khadijah da A’ishah da Hafsah, haka ma sauran ‘ya’yansa, kamar Su Zainab da Ruqayyah. Haka kuma lamarin ya ke game da Sahabban Manzon Allah (SAW), tun ma ba Halifofin da su ka biyo bayansa ba, wato, Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da kuma sauran Sahabbai.

Aqidar Shi’a ita kuma ta ginu ne akan wariya a tsakanin waxannan tsarkakakkun bayin Allah waxanda su ka samu tarbiyyarsu daga hannun Manzon Allah (SAW), a daidai lokacin da alqur’ani ya ke saukowa da ximinsa. ‘Yan Shi’ah sun rungumi iyalan gidan Manzon Allah ne kawai, su ka bar almajiransa. Kuma sun kitsa wasu irin tatsuniyoyi marasa tushe don su labarta cewa, wai akwai adawa da gaba a tsakaninsu.

Wannan bincike ya zo ne don fexe gaskiya game da lamarin, ya kuma soma da wannan tambaya, ita ce: “Su wane ne Masoyan Ahlulbaiti”? Don samar da amsarta kuwa, sai binciken ya fantsama a cikin mavuvvugar aqidun Sunnah da na Shi’ah a game da Ahlulbaiti ta yadda mai karatu da kansa daga qarshe zai bai wa kansa amsar wannan tambaya.

Malam Aliyu Rufa'i ya yi amfani da takardun binciken da kuma kaset kaset xin laccocin da aka gabatar da wannan binciken a wurare daban daban na jihohin Arewacin Najeriya. Don haka, aikin nasa ya fito mafi kusa da sigar da mai binciken zai iya fitowa da ita da shi ne ya fassara. Amma duk da haka, na sake nazarin aikin baki xaya, tare da komawa ga wasu daga cikin manazartar binciken don qara tantance sahihancinsu.

Ina roqon Allah ya saka ma sa da alherinsa, ya sa aikin ya zamo jagoran shiriya ga masu neman gaskiya.

Baban Ramlatu,

Muhammad Mansur Ibrahim

A Birnin Iskandariyyah, ta qasar Misra

Daren 14 ga Shawwal 1426B.H/ 15 ga Nuwamba 2005M


BABI NA XAYA

1.0 Iyalan Gidan Manzon Allah
Wannan babi zai yi bayani ne, a kan abinda kalmar ‘Iyali’ ke nufi, tare kuma da biyar daddagin jinsin mutanen da, ke iya shiga qarqashin tutar Iyalan gidan Manzon Allah (SAW) na daga danginsa, na wajen uwa da uba, matansa, ‘ya’yansa da zuri’arsa.
1.1 Ma’anar Iyalan Gida

Asali, kalmar iyali, a harshen Musulunci na nufin “matar mutum”. Iyalin mutum, na nufin matarsa. Kamar yadda Al-qur’ani mai tsarki da Sunnar Manzo Allah, suka nuna. Allah (SWT) na cewa akan Matar Annabi Musa (AS):

﴿ فَلَمَّا قَضَى مُوسَى الْأَجَلَ وَسَارَ بِأَهْلِهِ آَنَسَ مِنْ جَانِبِ الطُّورِ نَارًا قَالَ لِأَهْلِهِ امْكُثُوا إِنِّي آَنَسْتُ نَارًا لَعَلِّي آَتِيكُمْ مِنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ جَذْوَةٍ مِنَ النَّارِ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ (29)﴾ [سورة القصص]

Ma’ana:


To, a lokacin da Musa ya qare adadin, kuma yana tafiya da Iyalinsa (Matarsa), sai ya tsinkayi wata wuta daga gefen dutse (Xuri Sina’a). Ya ce wa Iyalansa (Matarsa),

“ku dakanta, lalle ne ni, na tsinkayi wata wuta, tsa-

mmanina ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani

labari, ko kuwa da guntun makamashi daga wutar

don ko kuji xumi”

[Suratul Qasas : 29]
Ya kuma ce a kan Annabi Ibrahim (AS) :

﴿هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَ الْمُكْرَمِينَ (24) إِذْ دَخَلُوا عَلَيْهِ فَقَالُوا سَلَامًا قَالَ سَلَامٌ قَوْمٌ مُنْكَرُونَ (25) فَرَاغَ إِلَى أَهْلِهِ فَجَاءَ بِعِجْلٍ سَمِينٍ (26) فَقَرَّبَهُ إِلَيْهِمْ قَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ (27)﴾ [سورة الذاريات].

Shin, Labarin baqin Ibrahim, waxanda aka girmama, ya zo maka ?. A lokacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce “Aminci ya tabbata a gare ku, mutane baqi !”. Sai ya juya zuwa ga Iyalansa, Sa’annan ya zo da maraqi tutturna. Sai Ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce”. Ba za ku Ci ba ?”

[Suratul Zariyati : 24-27]

A wata surar kuma, Al-qur’ani ya tabbatar da cewa, matar mutum, da yace daga cikin Iyalinsa kuma ya ba ta sunan (Ahlul Baiti) in da ya ce, a kan matar Annabi Ibrahim (AS):

﴿وَامْرَأَتُهُ قَائِمَةٌ فَضَحِكَتْ فَبَشَّرْنَاهَا بِإِسْحَاقَ وَمِنْ وَرَاءِ إِسْحَاقَ يَعْقُوبَ (71) قَالَتْ يَا وَيْلَتَى أَأَلِدُ وَأَنَا عَجُوزٌ وَهَذَا بَعْلِي شَيْخًا إِنَّ هَذَا لَشَيْءٌ عَجِيبٌ (72) قَالُوا أَتَعْجَبِينَ مِنْ أَمْرِ اللَّهِ رَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الْبَيْتِ إِنَّهُ حَمِيدٌ مَجِيدٌ (73)﴾ [سورة هود]

Kuma matarsa tana tsaye. Tayi dariya sai muka yi mata bushara (da haihuwar) Is’haqa, kuma a bayan Is’haqa, Yaquba. Sai ta ce, “ya kaitona ! shin zan haihu ne alhali kuwa ina tsohuwa, kuma ga mijina tsoho ne? Lalle wannan haqiqa, abu ne mai ban mamaki.” Suka ce kina mamaki ne daga al’amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarsa su tabbata a kanku, ya Ahlul Baiti (mutanen babban gida) ! Lalle ne shi abin godewa ne, mai girma.”[suratul Hud : 71 – 73]
Don haka, a lokacin da Manzon Allah (SAW) ya ke cewa: “mafi alherinku, shi ne, wanda ya fi kyautata wa iyalinsa. Ni kuwa ni ne zakara a cikinku ta wajen kyautata ma iyalina. Manzon Allah (SAW) ya na nuni ne zuwa ga kyautatawar da ya ke yi wa matansa.

A kan haka, iyalin gidan Manzon Allah (SAW) ke nan, su ne matansa a matakin farko. Haka kuma malamai sun yi bayani bisa ga wasu hujjoji da zamu faxe su nan gaba cewa, ‘ya’yansa, zuri’arsa da makusantansa (danginsa) waxanda aka haramta wa cin sadaka, saboda kusancinsu da shi, aka tanadar masu humusin humusin ganima (4/100) dukkansu suna cikin iyalan gidansa (Ahlulbaiti).

Ba wata tantama akan kasancewar matan Manzon Allah a cikin iyalansa idan mu ka yi nazarin ayoyin da Allah ya kira (Ahlulbaiti) a cikinsu. Ga su nan mai karatu sai ka duba su da kyau:
﴿ يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُلْ لِأَزْوَاجِكَ إِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا فَتَعَالَيْنَ أُمَتِّعْكُنَّ وَأُسَرِّحْكُنَّ سَرَاحًا جَمِيلًا (28) وَإِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَالدَّارَ الْآَخِرَةَ فَإِنَّ اللَّهَ أَعَدَّ لِلْمُحْسِنَاتِ مِنْكُنَّ أَجْرًا عَظِيمًا (29) يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ مَنْ يَأْتِ مِنْكُنَّ بِفَاحِشَةٍ مُبَيِّنَةٍ يُضَاعَفْ لَهَا الْعَذَابُ ضِعْفَيْنِ وَكَانَ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرًا (30) وَمَنْ يَقْنُتْ مِنْكُنَّ لِلَّهِ وَرَسُولِهِ وَتَعْمَلْ صَالِحًا نُؤْتِهَا أَجْرَهَا مَرَّتَيْنِ وَأَعْتَدْنَا لَهَا رِزْقًا كَرِيمًا (31) يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا (32) وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآَتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا (33) وَاذْكُرْنَ مَا يُتْلَى فِي بُيُوتِكُنَّ مِنْ آَيَاتِ اللَّهِ وَالْحِكْمَةِ إِنَّ اللَّهَ كَانَ لَطِيفًا خَبِيرًا (34)﴾. [سورة الأحزاب].
ya kai Annabi ! ka ce wa Matanka - , “Idan kun kasance kuna nufin rayuwar duniya da qawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwana, kuma in sake ku, saki mai kyau.” Kuma idan kun kasance kuna nufin Allah da Manzonsa da gidan Lahira, to, Lalle, Allah ya yi tattalin wani sakamako mai girma ga masu kyautatawa, daga gare ku.” Ya Mata nannabi ! wadda ta zo da alfasha bayyananna daga cikinku, za a ninka mata azaba ninki biyu. Kuma wancan ya kasance mai sauqi ga Allah. Kuma wadda ta yi tawali’u daga cikinku ga Allah da Manzonsa, kuma ta aikata aiki na qwarai, za mu ba ta sakamakonta ninki biyu, kuma mun yi mata tattalin arziki na karimci. Ya mata nannabi! Ba ku zama kamar kowa ba daga mata, idan kun yi taqawa, saboda haka kada ku sassautar da magana har wanda ke da cuta a cikin zuciyarsa ya yi xammani, kuma ku faxi magana ta alheri. Kuma ku tabbata a cikin gidajenku, kuma kada ku yi fitar gaye-gaye irin fitar gaye-gaye ta jahiliyyar farko kuma ku tsai da sallah, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi xa’a ga Allah da Manzonsa. Allah na nufin ne kawai ya tafiyar da qazanta daga gare ku, ya (Ahlulbaiti) Mutanen Babban Gida! kuma ya tsarkake ku, tsarkakewa. Kuma ku tuna abinda ake karantawa a cikin xakunanku daga ayoyin Allah da hukunci. Lalle Allah ya kasance mai tausasawa.

[suratul Ahzab : 28 – 34]

Manzon Allah da kansa ya kan kira matansa da sunan (Ahlulbaiti) kamar yadda za mu gani a cikin wannan Hadisi da Imamul Buhari ya ruwaito.

Daga Anas xan Malik (R.A) ya ce, Wata rana Manzon Allah (SAW) ya shiga xakin Sayyida A’ishah, bayan ya yi biko da matarsa Zainab ‘yar Jahshi, sai ya ce: Amincin Allah da rahamarsa su tabbata gare ku, ya ku (Ahlulbaiti) “mutanen Babban Gida”. Ta karva masa, ita A’ishahr, da cewa “ku ma amincin Allah da rahamarsa da albarkarsa su tabbata gare ku, ya kwanan amarya? Allah ya sa alheri”. Sa’annan sai ya ci gaba da lelleqa xakunan matansa, suna gaisuwa kamar yadda suka gaisa da sayyidah A’ishah (RA) yana faxa ma su abin da ya faxa mata, su kuma su na amsa ma sa kamar yadda ta amsa ma sa.1

Haka kuma, gaba xayan zuri’ar Manzon Allah (SAW) na daga cikin iyalansa. Za mu fahimci haka idan muka dubi Salatin Ibrahimiyyah wanda Manzon Allah ya koyar da Sahabbansa, ya na cewa:

اللهم صل على محمد وعلى أزواجه وذريته كما صليت على إبراهيم

وبارك على محمد وعلى أزواجه وذريته كما باركت على إبراهيم إنك حميد مجيد


“ku ce ya Ubangiji ka daxa tsira bisa ga Muhammadu da matansa da Zuri’arsa, kamar yadda ka daxa tsira bisa ga Ibrahim. Ka kuma yi albarka bisa ga Muhammadu da Matansa da Zuri’arsa, kamar yadda ka yi albarka bisa ga Ibrahim, Lalle kai ne Mai girma, abin godiya”.2 Wannan ya zo ne, a matsayin fassara ga abinda ya zo a ruwayar da tafi shahara kamar haka:

اللهم صل على محمد وعلى آل محمد

“Allahuma Salli Ala Muhammadin Wa Ala Ali Muhammadin…”.
Dangin Manzon Allah waxanda ke shiga a cikin Ahlulbaiti sun haxa da duk jinsin mutanen da Manzon Allah ya haramta ma su cin sadaqa saboda sun yi tarayya da shi a kakansa Abdul Muxxalib, kuma sun haxa da; Iyalin Aliyu da na jafaru da na Aqilu da na Abbas kamar yadda yazo a ruwayar Zaidu bin Arqam a cikin Sahihu Muslim.3 Wasu malamai ma sun sanya iyalan Harisu xan Abdul-muxallibi. Ga nasu dalilin:

An ruwaito cewa, Abdul-Muxxalibi xan Rabiatu xan Abbas xan Abdul-Muxxalibi, da Falalu xan Abbas xan Abdul Muxxalibi sun nemi Manzon Allah (SAW) su biyu, da ya xauke su aikin karvar Zakka domin su samu kamishon da ake bai wa masu karvarta daga cikinta. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce ma su: “Wannan Zakka da kuke gani, qazantar mutane ce, ba ta halatta ga Muhammadu da Iyalin gidansa.4 Wannan ya na ingantar da zaman Iyalan Harisu daga Ahlulbaiti, don shi ma xa ne ga Abdulmuxxalib.

Wannan da’irar tana daxa faxi idan muka leqa wasu nassoshin, kamar ruwayar da Xabarani da Haisami su ka kawo a littafansu cewa, a lokacin da wasu mata suka yi wa Durratu ‘yar Abu Lahabi xan Abdul Muxxalibi gorin cewa, Hijirarta, ba za ta amfane ta da komai ba, don Allah (SWT) ya yi tir da mahaifinta a cikin Al-qur’ani, Manzon Allah (SAW) ya sami wannan labari, sai ya qulla huxuba. A cikinta kuma yake cewa; A kan me za a cuta min ga xaya daga cikin Iyalaina, a yi mata gori?.5

Bisa ga haka ne, Malam Abbad ya ce: Duk musulmin da ya yi tarayya da Manzon Allah (SAW) a wajen kakansa Abdul Muxxalib to, yana cikin Ahlulbaiti kuma cin sadaka ya haramta gare shi.6


1.2 ‘Yan’uwan Haihuwar mahaifin Manzon Allah (SAW) Maza da Mata

Waxannan sun haxa da ‘ya’yan xakuna daban daban kamar haka:- 1. Harisu: Shi ne babbansu, da shi ne kuma ake yi wa Abu Xalib alkunya. Mahaifiyarsa ita ce Safiyyatu ‘yar Junaidibu.

 2. Yan’uwan mahaifin Manzon Allah (SAW) na uwa xaya uba xaya, guda biyar, da suka haxa da: Zubairu da Abu-Xalib da Arwa da Atika da Ummu Hakim al-Baidha’u (tagwan Abdullahi). Mahaifiyarsu itace Faximatu ‘yar Amru Al-makhzumiyya.

 3. Hamza da Muqawwamu da Safiyyatu. Mahaifiyarsu ita ce Halatu ‘yar Wahabi, wato da ita da Mahaifiyar Manzon Allah (SAW) xiyan wa da qanwa ne.

 4. Abbas da Darraru. Mahaifiyarsu ita ce Nutailatu ‘yar Janabizu.

 5. Abu Lahabi. Sunansa na yanka shi ne Abdul-Uzza. Mahaifiyarsa ita ce Lubna ‘yar Hijru Al-khuzaimiyyah.

Akwai kuma irin su Abdul-Ka’abati da Hajlu da Qusamu da Gaidaqu a cikin wannan ayari, amma a xan wannan bincike ba mu kai ga sanin iyayensu mata ba.

Huxu daga cikin waxannan ‘yan’uwa, na mahaifin Manzo Allah (SAW) ne, suka riski Musulunci, daga cikin maza. Wato; Hamza da Abbas da Abu-Xalib da Abu-Lahabi. Daga cikin mata kuma akwai guda uku. Wato; Safiyyatu da Arwa da Atika. Kuma matan gaba xaya sun musulunta; mazan kuwa sai aka yi raba dai dai, biyu suka ba da gaskiya, wato Hamza da Abbas (RA), biyu kuwa suka cije, wato; Abu-Xalib da Abu-Lahab. Banbancin da ke tsakaninsu kawai, shi ne, rashin bayar da gaskiyarsu bai hana, Abu-Xalib ya ba Manzon Allah (SAW) gagarumar gudammawa ba. savanin Abu-Lahabi, wanda ba shi ga maciji da Manzon Allah (SAW).

Sauran kuwa da ba su riski Musuluncin ba, sun haxa da : Harisu da Zubairu da Umaimatu da Ummu Hakim Al-Baidha’u da Barratu.
1.3 ‘Ya’yan ‘yan’uwan mahaifin Manzon Allah (SAW).

Babu abinda ya yi saura, daga cikin Zuri’ar Zubairu da Hamza. Amma Harisu da Abbas da Abu-Xalib da Abu-Lahabi duk zuri’arsu ta wanzu.

Ya’yan Hamza: Hamza ya haifi ‘ya’ya takwas (8) biyar (5) Maza, da suka haxa da : Ya’ala da Ammaru da Umaru da Amiru sai Uku (3) Mata; Ummul-Fadhli da faximatu da Umamatu.

Babban xan Hamza, Ya’ala ne kawai ya rayu, har ya haifi ‘ya’ya Maza guda biyar (5) waxanda kuma Allah bai yi wa tsawon kwanukka ba.

Ya’yan Abbas: Abbas ya haifi ‘ya’ya goma sha Huxu (14) goma (10) maza, huxu (4) Mata. Sun haxa da; Fadhlu da Abdullahi da Qusamu su ne manyan ‘ya’yansa, da Ubaidullahi da Ma’abad da Abdurrahman. Mahaifiyarsu ita ce, Ummul Fadhli, Lubabatul-Kubra, (yar Ummul-Muminina Maimunatu ‘yar Harisu,) Al-Hilaliyyah. Wadda ke da ‘yar ’uwa mai suna, Lubabatus-Sugra, mahaifiyar Khalidu xan Walidu. Sai kuma Harisu da Qusamu da Aunu da Tammam, su kuwa mahaifiyarsu Barumiya ce (wadda aka zo da ita daga qasar Rum). Duk waxannan ‘ya’ya na Abbas sun sadu da Manzon Allah (SAW). Har babbansu ma da mai bi masa, sun ruwaito Hadissai daga Manzo kai tsaye. Na biyun ma shi ne Manzon Allah (SAW) ya yi wa addu’ar laqantar Al-qur’ani da Tafsiri. Shi ne kuma kakan halifofi Abbasiyyawa. Matan kuwa su ne; Ummu Habib da Aminatu da Safiyyatu da Ummul – Fadhli.

Ya’yan Abu-Xalib: Abu-Xalib shi ya haifi Aliyu da Ja’afaru da Aqilu da Jumanah da Ummu Hani’i, zanannen sunanta kuwa shi ne Fakhitah. Mahaifiyarsu ita ce Faximatu ‘yar Asad xan Hashimu. Ta kuma riski Manzon Allah (SAW).

Ya’yan Abu Lahabi: Ya haifi Durratu wacce labarinta ya gabata.

Ya’yan Safiyyatu: Ita kuma Safiyyatu ‘yar Abdul-Muxxalibi, ita ce mahaifiyar Zubairu xan Auwamu, xayan waxanda aka yi wa bushara da Aljanna. Zubairu kuwa shi ne wanda ya Auri Asma’u ‘yar Sayyadi Abubakar as-Siddiqu, suka haifi Abdullahi xan Zubairu, wanda yake shi da baban nasa da Umminsa da babanta da kakanta duk, Sahabbai ne (RA). Daga cikin ‘ya’yan Safiyyatu kuma akwai As-Sa’ibul – Badri.

ya’yan Umaimatu: An yi savani a cikin, riskuwarta ga musulunci. Amma ‘ya’yanta guda shidda (6), duk sun musulunta babu shakka. Uku daga cikinsu maza ne; Shahidu, Abdullahi Al-Mujada’ da Muhajiru, Abdullahi, Abu Ahmad al’A’ama da Ubaidullahi xan Jahshu mijin Ramlatu na farko kafin Manzon Allah (SAW) ya aure ta. Uku kuwa mata ne waxanda kuma suka musulunta da wuri har su ka yi hijira sau biyu. Su ne; Zainab Ummul-Muminina da Hamnatu da Ummu Habibah.

ya’yan Arwa: Ita kuma Arwa ita ce mahaifiyar Xulaibu xan Umaru, wanda ya na daga cikin Sahabai.

ya’yan Atika: Atika ta auri Abu-Ummayyah xan Magirata Al-makhzumi, suka haifi ; Abdullahi da zubairu da Ummul-Mumunina, Ummu Salamah.

ya’yan Barratu: Ita kuma Barratu ita ta haifi Abu Salamah (RA) mijin Ummu Salamah kafin ya rasu Manzon Allah (SAW) ya aure ta. Haka kuma ita ta haifi sahabi Abu Sabrata.

ya’yan Ummu hakim, Al-Baidha’u: ita ce tagwan mahaifin Manzon Allah (SAW) wadda aka haife su rana xaya da shi. Ita ce kuma Kakar Sayyiduna Usman xan Affana (RA) mahaifiyar uwarsa Arwa xiyar kuraizu.

Mu kula:

Daga abin da ya gabata, muna iya lura cewa, • Iyayen Mummunai Ummu Salamah (xiyar Atika) da Zainab ‘yar Jahshu (xiyar Umaimatu) duk taubashinnen Manzon Allah (SAW) ne, (xan macce da xan namiji) ‘ya’yan gwaggwanninsa.

 • Ali xan Abu xalib a matsayin qanen Manzon Allah (SAW) ne, domin da mahaifinsa da na Manzon Allah (SAW) wa da qani ne. Ita kuma Fatimah, matarsa, a matsayin ‘ya ta ke a wurinsa.

 • Sayyiduna Usman (RA) a matsayin xa yake ga Manzon Allah (SAW), domin jikan gwaggonsa ne. Daga nan za mu fahimci cewa, ‘ya’yan Manzon Allah (SAW) da ya aura Ruqayyah da Ummu Kulsum, a matsayin qannensa ne na zumunta.

 • Uwar gidan Baffan Manzon Allah (SAW), Abbas xan Abdul Muxxalibi, ina nufin Lubabatul Kubra yar Matar Manzon Allah (SAW) ce Maimunatu ‘yar Harisu.

 • Shi kuma Khalid xan Walid (RA) xa ne ga Manzon Allah (SAW) ta wajen Uwar Mummunai Maimunatu, domin qanwar uwarsa ce.

 • Ummu Hani’i (RA) wadda Manzon Allah (SAW) ya ke ziyarta a Ajyad, har ma wasu ruwayoyi su ka nuna cewa, daga gidanta ne aka yi Isra’i da shi, a matsayin qanwarsa ta ke, ‘yar baffansa, Abu xalib, kuma yar Sayyiduna Ali (RA).

 • Abdullahi xan Abbas da qanensa Fadlu duk da yake qannen Manzon Allah (SAW) ne ta wajen mahaifinsu, amma kuma ‘ya’yansa ne ta wajen matarsa Maimunatu, qanwar mahaifiyarsu.

 • Abu Salamah (RA) wanda Manzon Allah (SAW) ya auri matarsa a bayan rasuwarsa Ummu Salamah, a matsayin qanin Manzon Allah (SAW) ya ke, xan gwaggonsa Barratu.

 • Haka shi ma Ubaidullahi xan Jahshu, wanda Manzon Allah (SAW) ya auri matarsa Ramlatu a bayan rasuwarsa, taubashin Manzon Allah (SAW) ne, xan gwaggonsa Umaimatu. Haka kuma shi ne wan matarsa Zainab xiyar Jahshu.

 • Zubairu xan Awwamu wanda ya auri Asma’u xiyar Sayyiduna Abubakar kuma yar matar Manzon Allah (SAW) A’ishah, shi ma taubashin Manzon Allah (SAW) ne, xan gwaggonsa Safiyyatu.


1.4 Kawunnen Manzon Allah (SAW) (‘Yan’uwan haihuwar Mahaifiyarsa):

Aminatu xiyar Wahabu, mahaifiyar Manzon Allah (SAW) na da ‘yan uwan haihuwa guda biyar (5) Maza, da suka haxa da: 1. Al Aswadu xan Wahabu, ya musulunta, ya abokanci Manzon Allah (SAW), ya kuma ruwaito Hadisai daga gare shi.

 2. Abdullahi xan wahabu: ya musulunta ranar da aka ci garin Makkah.

 3. Umaru xan Wahabu: Ba cikakken labarinsa.

 4. Abdu Yagusa xan Wahabu: Shi ne mafi shahara daga cikin kawunnen Manzon Allah (SAW). Bai riski Manzanci ba. Daga cikin zuri’arsa, akwai Al-Aswad xan Abdu Yagusa – ya mutu mushiriki, yana kuma mai tsananin tozartawa ga Manzon Allah (SAW). Sai dai ya haifi ‘ya’ya Musulmai, waxanda su ka abokanci Manzon Allah (SAW) su ne; Abdurrahman da Khalidatu. Haka kuma ya na da xa mushriki mai suna, Arqamu xan Abdu yagusa, shi kuma wannan yana da xa mai suna Abdullahi xan Arqamu, wanda ya musulunta, ya abokanci Manzon Allah (SAW).

 5. Khalafu xan Wahabu: Yana da xa mai suna Al-Aswadu xan khalafu, sahabi ne, kuma ya yo ruwaya daga Manzon Allah (SAW).

Haka kuma Amina tana da ‘yan’uwan haihuwa mata, guda huxu (4) da suka haxa da:

 1. Fakhita ‘yar Amiru

 2. Furai’atu ‘yar Wahabu

 3. Uqailatu ‘yar kumainu

 4. Ummu Abdin, mahaifiyar Abdullahi xan Mas’ud

Tabbataciyar magana dai ita ce, dukan matan nan, danginta ne daga qabilar Bani Zuhrah dangin mahaifinta, amma ba abokan haihuwarta ba ne. Sai fa Uqailatu ‘yar kumainu, ita kam, ‘yar’uwar Aminatu ce ta wajen uwa, amma ba su haxa uba ba. Akan haka, ita ce Inna ta ainihi ga Manzon Allah (SAW).
Share with your friends:
  1   2   3   4   5


The database is protected by copyright ©dentisty.org 2019
send message

    Main page